Amfanin suratu yasin
Suratu Yasin, daya daga cikin surorin Al-Qur’ani mai tsarki, tana da matukar muhimmanci a rayuwar Musulmi.
Wannan sura, wacce take cikin Juzu’u na 23, tana kunshe da sakonni masu karfi wadanda suke taimakawa wajen karfafa imani da ciyar da rayuwar Musulmi gaba daya.
A sani cewa Suratul Yasin ba tada Wani Girma ko fifiko akan Sauran surorin Alqurani, Babu wata hadisi ingantace dake nuna fifikon ta akan Sauran surori
Duk da haka ita sura ce a cikin Alqurani Kuma ana iya karantata da niyya kuma tawwasulin da ita kamar yadda shari'ar ta Fada kuma za'a iya yin hakan akan Sauran sororin cikin Alqurani
Baya ga haka ga jerin Wasu surori wadanda aka sumu nassi na hadisi bisa ingancin su ga Mai Karantata Yana Mai Imani da Takawa
1. Suratul Fatiha (Ummul Kitab)
Suratul Fatiha, wacc...








