Hukumar EFCC Ta Gurfanar da Tsohon Gwamnan Jihar Kogi a Gaban Kotu a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja. Wannan lamari ya faru ne bayan Yahaya Bello ya shafe wani lokaci yana ɓoye daga hukumar, wanda ya jawo hankalin jama'a.A ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba, 2024, Yahaya Bello ya miƙa kansa ga jami'an EFCC a hedkwatarsu da misalin ƙarfe 12:55 na rana. Wannan mika kansa ya biyo bayan nemar da hukumar ta yi a baya, inda aka ayyana cewa tana neman tsohon gwamnan bisa zargin ƙin mutunta gayyatar da aka yi masa. A baya, hukuma ta ci gaba da shari'a ba tare da ya bayyana a gaban kotu ba.EFCC na tuhumar Yahaya Bello da aikata laifuffuka da suka shafi karkatar da kuɗi a lokacin da yake mulki, inda aka zarge shi da wawure maƙudan kudi da suka kai N80.2 billion...








