Zuwan Tinubu Faris: Najeriya ta Kulla Yarjejeniyar Ma’adanai da Faransa
Najeriya da Faransa sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa don inganta ma'adanai masu muhimmanci, musamman tagulla. Yarjejeniyar ta shafi bincike, horo, da musayar dalibai domin inganta fasaha da kwarewa a fannin ma'adanai.Ana fatan za a rage illar da hakar ma'adanai ke yi wa muhalli da kuma gyara ramuka da aka bari a Najeriya. Yarjejeniyar ta kunshi inganta amfani da ma’adanai kamar tagulla ta hanyar fasahar makamashi mai tsafta.Ministan ma'adanai, Dr. Dele Alake, wanda ya sanya hannu a madadin Najeriya, ya bayyana cewa wannan mataki zai kawo ci gaba mai dorewa a fannin ma’adanai. Yarjejeniyar ta haɗa da:Za a horas da dalibai a fannin ma'adanai, tare da gudanar da taron karawa juna sani akai-akai domin inganta kwarewar ma'aikata.Dr. Alake ya bayyana wannan yarjejeniya a matsayin babbar ...








