
Hawan Sallah: Sanusi II Ya Dau Zafi, Ya Yi Addu’o’i kan Masu Son Tayar da Tarzoma a Kano
Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga al'ummar jihar Kano da su kwantar da hankulansu tare da guje wa tayar da tarzoma. A cikin addu'o'in da ya yi, Sanusi II ya roƙi Allah ya mayar wa masu son tayar da fitina a jihar da aniyarsu.A cikin wani bidiyo da masarautar Kano ta fitar, Sanusi II ya yi addu'o'in samun zaman lafiya a jihar, wacce ta kasance a cikin halin rashin tabbas saboda rigimar sarauta tsakanin sarakunan biyu. Ya yi kira ga al'ummar Kano da su tankawa duk wanda ya takale su da faɗa, yana mai jaddada cewa halayyar mutanen da aka yi nasara a kansu ne.Sarkin na Kano ya yi addu'o'in cewa, "Duk wanda yake neman ya hura wuta a Kano, Allah ya sa wutar ta ƙone shi," tare da jaddada cewa mutane su ci gaba da yin addu'o'i, musamman a watan Ramadan.A yanzu haka, akwai damuwa game da yiwuwar h...