
Majalisar Dattijai Ta karyata Maganganun Pastor Bakare Kan Dokar Gaggawa da Dakatarwa
Majalisar Dattijai ta Najeriya ta musanta maganganun Pastor Tunde Bakare kan rawar da Majalisar ke takawa wajen bayyana dokar gaggawa a Jihar Rivers da kuma Dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Kogi ta Tsakiya.
Majalisar ta bayyana cewa maganganun Bakare suna dauke da kuskure tare da cewar suna dauke da "zarge-zarge marasa tushe." A cikin jawabin da aka fitar, shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar, Yemi Adaramodu, ya jaddada cewa yayin da Majalisar ke girmama hakkin 'yan kasa na bayyana ra'ayoyi, ba za ta zura ido ba idan maganganun sun wuce iyaka.
Bakare, wanda shine shugaban The Citadel Global Community Church, ya yi suka kan Dakatar da Akpoti-Uduaghan da kuma amincewar shugaban kasa Bola Tinubu akan dokar gaggawa a Rivers, yana zargin shugabannin Najeriya da ƙoƙari...