Atiku Ya Yi Zargi Kan Bashin N40trn da Tinubu Ke Shirin Karɓowa

Dan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan shirin gwamnatin Bola Tinubu na karɓar bashin Naira tiriliyan 40. Atiku ya yi wannan zargi a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa wannan bashin na da nufin kamfen na zaɓen 2027.

Ya yi zargin cewa Tinubu na shirin amfani da wannan rance ne domin cike gibin kasafin kuɗi da ba a bayyana ba, da kuma gina titin gaɓar teku. A cewarsa, wannan yunkuri na nuna cewa gwamnatin Tinubu ba ta damu da talakawa ba, inda ya jaddada cewa cire tallafin wutar lantarki, man fetur, da ilimi yana shafar mutane masu rauni.

Atiku ya jero abubuwa guda uku da Tinubu zai yi da wannan bashin, wanda ya haɗa da:

1. Kuɗin yakin neman zaɓe
2. Cike gibin kasafin kuɗin da ba a bayyana ba
3. Naira tiriliyan 15 don gina titin gaɓar teku

Wannan zargi na Atiku ya jawo cece-kuce a cikin al’umma, inda wasu suka goyi bayan ra’ayinsa, yayin da wasu ke ganin wannan yunkuri na siyasa ne kawai. Ana sa ran ganin yadda wannan lamari zai shafi zaben 2027 da sauran al’amuran siyasa a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *