Atiku Abubakar na Shirin  Barin Jam’iyyar PDP?

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa na Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana rahotannin da ke cewa yana shirin barin jam’iyyar PDP a matsayin ƙarya maras tushe. A cikin sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya fitar a ranar Asabar, 8 ga watan Maris, 2025, Atiku ya tabbatar da cewa har yanzu shi cikakken mamba ne na jam’iyyar PDP.

Atiku ya nuna aniyarsa ta ganin an samu gagarumar haɗaka wacce za ta kawar da jam’iyyar APC a zaben 2027. Ya ce, “Mun lura da cewa wasu kafafen yaɗa labarai na yaɗa labaran da ba su da tushe kan cewa zan bar jam’iyyar PDP.”

Ya ƙara da cewa wannan jita-jita ta ci karo da manufar haɗakar jam’iyyun adawa da yake jagoranta, wacce ta haɗa har da PDP. Atiku ya bayyana cewa yana ƙoƙarin samar da babbar haɗaka wacce za ta haɗa dukkanin jam’iyyun adawa, domin kawo sauƙi ga al’umma.

Haka zalika, akwai rahotannin da suka bayyana cewa wasu ƙungiyoyin goyon bayan Atiku sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, amma Atiku ya ci gaba da jaddada cewa har yanzu yana da niyyar ci gaba da aiki tare da PDP.

Wannan bayani ya zo a lokacin da ake ta jita-jitar cewa Atiku na shirin barin jam’iyyar domin shiryawa zaben shugaban ƙasa na 2027. Duk da haka, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya musanta wannan zargi, yana mai cewa yana da burin haɗa kai tare da sauran manyan ƴan siyasa don samun nasara a gaba.