Asalin Kungiyar Lakurawa da Yadda Suka Shigo Najeriya

An gano cewa kungiyar Lakurawa, wacce ta shahara wajen aikata ta’addanci a arewacin Najeriya, ta fara ne a shekarar 1997 a Nijar, a karkashin shugabancin Ibrahim Baré Maïnassara. An kafa kungiyar ne don kare makiyaya daga hare-haren ‘yan fashi da ke yawan kutsawa daga Mali.

A lokacin, ‘yan fashi suna yawan satar dabbobi, wanda hakan ya jefa makiyaya cikin hatsari. Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar kafa kungiyar Lakurawa domin tunkarar wannan barazana. An bai wa mambobin kungiyar horo na soja da makamai domin tabbatar da tsaro a yankin.

Bayan nasarorin da Lakurawa suka yi wajen fatattakar ‘yan fashi daga Nijar, Shugaba Baré ya fadada shirin, inda aka kafa karin sansanonin horo a wasu wurare. Duk da haka, bayan rasuwar Shugaba Baré a shekarar 1999, makomar kungiyar ta fara zama mai cike da rashin tabbas.

A cikin shekarun da suka biyo baya, kungiyar ta fuskanci kalubale daga gwamnatin Nijar, wanda hakan ya haifar da rarrabuwar kawuna, inda wasu daga cikin mambobin kungiyar suka arce zuwa Najeriya. A Najeriya, sun sami karbuwa saboda tsayuwarsu kan yaki da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane, amma daga baya sun fara bayyana a matsayin ‘yan jihadi.

Bayan ficewar gwamnatin Libya a shekarar 2011, wasu daga cikin Lakurawa sun koma cikin kungiyar MUJAO a Mali. A shekarar 2013, bayan hare-haren sojin Faransa a arewacin Mali, wasu daga cikin wadannan mayakan sun tsere zuwa Nijar da Arewacin Najeriya.

Hakan ya sa gwamnatin Najeriya ta dauki mataki a kan sansanonin Lakurawa, tare da kaddamar da farmaki na soji a kan su a watan Disamba 2024. A cikin wannan farmaki, an yi nasarar shawo kan wasu daga cikin mayakan kungiyar.

Ko da yake kungiyar na ci gaba da aikata ta’addanci, gwamnatin Najeriya na kokarin dakile tasirinsu domin tabbatar da tsaro a yankin. Wannan lamari na nuna yadda kungiyar Lakurawa ta canza daga wata kungiyar tsaro zuwa kungiyar da ke aikata ta’addanci a Najeriya.