APC Ta Yi magana ka Shigar Kwankwaso Jam’iyyar

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta karyata rade-radin da ake yadawa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), na shirin komawa jam’iyyar mai mulki.

Jita-jitar ta yi ƙarfi musamman bayan murabus din Abdullahi Ganduje daga muƙamin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.  Sai dai a wata tattaunawa da Channels Television a ranar Lahadi, Sakataren Yaɗa Labaran APC na Ƙasa, Felix Morka, ya musanta wannan batu, yana mai cewa babu wata tattaunawa da ake yi tsakanin jam’iyyar da Kwankwaso kan batun shigarsa APC.

“Jam’iyyar da nake magana a madata ba ta ce komai ba game da yiwuwar Kwankwaso ya shigo,” in ji shi lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar tsohon gwamnan Kano ya sauya sheƙa.

Ya ƙara da cewa, “Ba mu yanke wani hukunci ba kuma ba za mu iya yanke shi a yanzu ba.”

Morka ya kuma yi watsi da ikirarin da ake yadawa game da wasu matsaloli a cikin gidan jam’iyyar, yana mai cewa APC na tafiya yadda ya kamata. Ya ce mutane na da ‘yancin faɗin abin da suke so, amma hakan ba yana nufin akwai matsala a jam’iyyar ba.

“Jam’iyya na gudana kamar yadda ya kamata. Mutane suna da ‘yancin yin abin da suke so, amma hakan ba ya nuna rashin aiki,” in ji shi.