“An Yi Babban Rashi”: Mahaifin Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Rasu

Allah ya yi wa Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero rasuwa. Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana wannan labari a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025.

Uba Sani ya tura sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, inda ya bayyana shi a matsayin dattijo mai addini da ya yi wa al’umma hidima. Gwamnan ya ce, “Rasuwar Ramalan Yero babbar rashi ce ga Masarautar Zazzau.”

Marigayin, wanda ya riƙe sarautar Turakin Dawakin Zazzau, yana daga cikin fitattun dattawan jihar da suka taka rawar gani a zamantakewa da addini. Gwamna Uba Sani ya yi addu’ar Allah ya yafe masa kura-kuransa kuma ya sa shi a cikin Aljannatul Firdaus.

Alhaji Ramalan Yero ya rasu bayan shafe shekaru yana yi wa al’umma hidima, kuma wannan rashi ya jawo babban alhini a tsakanin al’ummar jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *