An Sanya Ranar Fara Zanga-Zangar Adawa da Gwamnatin Tinubu

Kungiyar #EndBadGovernance ta sanar da shirin gudanar da zanga-zanga a ranar 12 ga Yuni, 2025, don nuna bacin ran ‘yan Najeriya kan gwamnatin Bola Tinubu.

Shugaban kungiyar, Comrade Hassan Soweto, ya bayyana a Legas cewa cire tallafin mai da faduwar Naira sun jefa miliyoyin mutane cikin talauci, inda tsadar abinci ta zarce kashi 40.

Soweto ya ce zanga-zangar za ta kasance a ranar da aka yi bikin dimokuradiyya, yana mai jaddada cewa mulkin Tinubu ya haifar da bala’i ga al’umma. Ya yi kira ga jami’an tsaro su tabbatar da zaman lafiya yayin zanga-zangar, yana mai zargin gwamnati da take hakkin dimokuradiyya.

Ya ce: “A yau ‘yan Najeriya suna rayuwa kamar bayi, inda ‘yancin fadin albarkacin baki da na siyasa an soke su baki daya.”

Kungiyar ta kuma bukaci hukunta jami’an tsaro da suka zalunta masu zanga-zanga a shekarar 2024, tare da bayar da diyya ga iyalan wadanda aka kashe.

Zanga-zangar ta na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar matsaloli da dama, ciki har da tsadar rayuwa da rashin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *