
Wata kotun Shari’a da ke Rigasa a jihar Kaduna ta raba wasu masoya biyu, Salisu Salele da Bilkisu Lawal, bayan da kotun ta haramtawa Salisu zuwa unguwarsu Bilkisu, ko kuma yin wata hulɗa da ita. Hukuncin ya biyo bayan korafin da iyayen Bilkisu suka shigar a gaban kotun, suna neman a raba ɗansu da Salisu.
Alƙalin kotun, Malam Salisu Abubakar-Tureta, ya yanke hukuncin bayan masoyan sun amince su rabu a gaban iyayensu da kuma shugaban unguwar. Daga ranar da aka yanke hukuncin, Salisu ba zai sake zuwa layinsu Bilkisu ba, ko kuma ya kirata a waya. Yin hakan zai jawo masa fushin hukuma.
“Daga yau, Salisu ba zai kira ko gana da Bilkisu ba, an hana shi bin unguwarsu ko tsayawa kusa da gidan su Bilkisu,” in ji alkalin. “In an kama shi yana kiranta ko ganinta a ko’ina, za a ɗauki matakin da ya dace a kansa.”
Mahaifiyar Bilkisu, Raliya Lawal, ce ta shigar da ƙarar a kotu, tana neman a raba ɗiyar tata da Salisu. Ta bayyana cewa Salisu yana zuwa wajen ɗiyar tata ba tare da izininsu ba. Duk da cewa ta kai ƙararta ga mahaifiyar Salisu, amma ba a ɗauki wani mataki ba. Salisu ya ci gaba da kiranta a waya, yana neman ganawa da ita a ɓoye. Raliya ta ce ta garzaya kotu ne saboda tana tsoron Salisu ya ɓata tarbiyyar ɗiyar tata.
A nasa ɓangaren, Salisu ya bayyana cewa yana son Bilkisu, amma ba zai iya aurenta ba yanzu saboda yana karatu a jami’a kuma ba shi da kuɗin sadaki. Ya ce yana fatan auren Bilkisu ne nan da shekaru biyu masu zuwa.
Wannan hukuncin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, inda wasu ke goyon bayan hukuncin kotun, wasu kuma na ganin an yi wa masoyan rashin adalci.