An Kaure da Fada da Akpabio a Majalisa kan Fifita Sanatocin Arewa? Gaskiya Ta Fito

An Kaure da Fada da Akpabio a Majalisa kan Fifita Sanatocin Arewa? Gaskiya Ta Fito

An yi ta yada jita-jita cewa an kaure da fada tsakanin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Opeyemi Bamidele a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024.

Wani mai amfani da kafar X, Jackson Ude, ya wallafa cewa Bamidele ya zargi Akpabio da nuna wariya ga Sanatocin Kudu wurin ba da shugabancin manyan kwamitoci.

Ude ya ce Bamidele ya ce Akpabio na ba da manyan kwamitoci ga abokansa da ke Arewacin Najeriya inda da yake fifita su fiye da sanatocin Kudu.

Sai dai Sanata Bamidele ya yi watsi da lamarin a shafin Facebook inda ya ce wanda ya yada labarin ya saba batawa mutane suna.

Sanarwar ta ce babu gaskiya kan rigima tsakanin Akpabio da Sanata Bamidele a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024.

Bamidele ya bukaci al’umma su yi watsi da jita-jitar inda ya ce an yi haka ne domin kawo sabani a tsakaninsu.
Haka nan, Akpabio ya yi kira ga jama’a su kaurace wa irin wadannan rahotanni na karya, yana mai cewa suna kokari ne don wargaza zaman lafiya da hadin kai na shugabannin majalisar.