An Kama wani da ake tuhuma da yin kudin jini da Dan danuwansa

Hukumar ‘yan sandan jihar Ekiti ta kama wani matashi mai shekaru 23, wanda aka bayyana da sunan Solomon Fabiyi, bisa zarginsa da yiwa dan danuwansa mai shekara bakwai, Jomiloju, shirin amfani dashi nayin kudin jini.

Mai magana da yawun hukumar, Sunday Abutu, ya fitar da sanarwa a ranar Talata, inda ya bayyana cewa an kama Fabiyi a ranar Jumma’a, 14 ga Fabrairu 2025, kafin ya yi amfani da dan danuwansa. Abutu ya ce, “An kama shi a lokacin da yake kan hanya don yin wannan mummunan aiki.”

Fabiyi ya amsa laifin a cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, inda ya bayyana cewa wani mai magani na gida ya umurce shi da ya nemo wani don wanan aikin. An ce mai maganin ya tabbatar masa cewa dan danuwansa ba zai mutu ba, amma zai kamu da wata cuta.

Duk da haka, a cikin wani abu mai ban mamaki, wannan mai magani ne ya sanar da ‘yan sanda lokacin da Fabiyi ya kawo yaron don aikata wannan mummunan aikin, wanda yayi sanadiyan kama shi

Wannan lamari na Fabiyi ya zo ne a cikin yanayi na rashin tsaro a jihar, bayan wani matashi mai shekaru 29, Abdulrahman Mohammed Bello, da aka kama saboda kisan gilla da ya yi wa wata dalibar Jami’a, Lawal Hafsah Yetunde, saboda dalilan kudin jini.