An Kama Babban Jagoran Ƴan Bindiga a Akwa Ibom

Rundunar ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom ta samu gagarumar nasara bayan ta kai samame kan wata ƙungiya mai garkuwa da mutane. A yayin wannan samame, an kashe mutum guda daga cikin ƴan bindigar, an kuma kama wasu tare da kwace makamai da miliyoyin kuɗi a hannunsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Timfon John, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun samu bayanan sirri kafin su kai harin a maboyar ƴan ta’addan da ke yankin Ikpe Annang, Ikpe Ikot Akpan, da Ikot Inyang a ƙaramar hukumar Essien Udim.

A lokacin da jami’an tsaro suka iso, ƴan bindigar sun yi ƙoƙarin tserewa ta hanyar bude wuta, amma jami’an tsaron sun mayar da martani. A cikin gumurzun, an ji wa ƴan bindigar biyar raunuka, inda aka garzaya da su asibiti, amma ɗaya daga cikin su ya rasu.

Bayan an kammala farmakin, jami’an tsaro sun kwato makamai da dama, ciki har da bindiga kirar AK-47, bindigar G3, da wasu kayayyaki kamar jaka cike da ƙifi da na’urar ƙara amo. Haka kuma, an kwato kuɗi sama da Naira miliyan 3 daga hannun ƴan ta’addan.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Akwa Ibom, Baba Azare, ya jinjinawa jami’an tsaro bisa kwazon da suka nuna a wannan aiki, ya kuma gargadi sauran ƴan ta’adda da ke addabar jihar cewa ba za su tsira daga hukuncin doka ba.

Ya ce, “Jihar Akwa Ibom ba za ta ƙara zama mafakar ƴan ta’adda ba. Za mu ci gaba da farautarsu har sai mun kawar da su gaba ɗaya.” Wannan nasara ta nuna jajircewar rundunar ‘yan sanda wajen tabbatar da tsaro a jihar.