Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

An Gano Motar Ɗan Majalisar da Ƴan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Shi

Rundunar ƴan sanda a jihar Anambra ta tabbatar da gano motar ɗan Majalisar dokokin jihar, Hon. Justice Azuka, wanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi. Kakakin rundunar, Tochukwu Ikenga, ya bayyana cewa suna ci gaba da kokarin ceto ɗan majalisar.

An yi garkuwa da Mista Azuka a daren ranar Talata a kan titin Ugwunapampa a karamar hukumar Onitsha ta Arewa, yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida domin shagulgulan Kirsimeti.

Dakarun ƴan sanda sun gano motar a gefen titin Upper Iweka, mai nisan kilomita da dama daga inda harin ya faru. Gano motar ya biyo bayan matakan da dakarun suka ɗauka domin ceto Hon Azuka cikin ƙoshin lafiya.

Kwamishinan yan sandan jihar Anambra, Nnaghe Obono, ya bukaci ƴan sandan da aka tura su kara kaimi wajen ceto dan majalisar da aka sace. Wannan lamarin ya jawo hankalin al’umma, suna rokon hukumomi su ɗauki matakin gaggawa wajen tabbatar da tsaron dukkanin mutane a jihar.