An Bukaci Yan Arewa Su Yi Watsi da Kwankwaso Kan Taɓa Tinubu

Wata kungiyar magoya bayan shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, NAT ta yi martani ga Sanata Rabi’u Kwankwaso kan sukar kudirin haraji.

Kungiyar ta yi kira ga yan Arewa da su yi watsi da maganganun da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi na sukar sauya fasalin harajin Najeriya.

A karon farko, madugun Kwankwasiyya ya soki kudirin harajin Shugaba Bola  Ahmad Tinubu ne a wani taron yaye ɗalibai a jami’ar Skyline ta jihar Kano.

NAT ta ce Kwankwaso bai kyauta ba da ya soki kudirin harajin a gaban dalibai. Kungiya ta yi raddi ga Kwankwaso kan sukar Tinubu.

Vanguard ta wallafa cewa kungiyar ta ce kamata ya yi Kwankwaso ya yi wa daliban bayanin mai kyau a kan dokar harajin maimakon suka.

” Shugaban kasa Bola Tinubu ya kawo kudirin haraji ne domin tabbatar da cigaba a Najeriya, ciki har da jihohin Arewa. Abin takaici ne yadda Kwankwaso ya tsaya a gaban ɗalibai yana ce musu Tinubu na son ruguza tattalin Arewa. Muna kira ga al’ummar Arewa da su yi watsi da maganganun Kwankwaso na sukar sauya fasalin haraji.” – Ƙungiyar NAT

Tribune ta wallafa cewa NAT ta ce sauya fasalin haraji abu ne mai muhimmanci da zai haɓaka tattalin kasa kuma ya kamata a goyi bayansa.

A karshe, yan kungiyar sun ce kamata ya yi a yabawa Bola Tinubu kan sauya fasalin haraji maimakon caccakarsa.