
Dillalan man fetur da kwararru a masana’antar man fetur sun yi hasashen cewa a shekarar 2025, farashin man fetur zai iya sauka zuwa N500 a kowace lita. Wannan hasashen ya biyo bayan dawowar aikin matatun man fetur na Port Harcourt da Warri, wanda zai taimaka wajen rage farashin man a Najeriya.
A halin yanzu, farashin man fetur yana tsakanin N900 da N950 a kowace lita a yawancin gidajen mai. Kwararru sun bayyana cewa, idan matatun man fetur sun fara samar da kayayyakin man fetur cikin lokaci, zai karfafa gasa a kasuwa da kuma rage farashi.
Sakataren yada labarai na Kungiyar Masu Siyar da Man Fetur Najeriya (IPMAN) ya bayyana cewa dawowa bakin aiki da wadannan matatun man fetur zai kawo canji mai kyau a kasuwar man fetur. Hakan zai bada damar samar da man fetur da yawa a cikin gida, wanda zai rage dogaro ga kayayyakin da ake shigo dasu daga waje.
A cewar masu ruwa da tsaki, tsarin naira-da-man fetur da kuma karuwar gasa a fannin samar da man fetur suna daga cikin abubuwan da zasu taimaka wajen rage farashin. Hakan na nufin cewa, ‘yan Najeriya za su fara jin dadin farashin man fetur mai rahusa a cikin wannan shekarar.
Shugaban kungiyar mai ta PETROAN ya amince da wannan hasashen, yana mai cewa farashin man fetur mai sauki zai zama wata dama ga ‘yan Najeriya a shekarar 2025. Wannan ci gaban na da alaka da yunkurin gwamnatin tarayya na inganta bangaren man fetur da rage matsalolin da ke shafar farashin kayayyaki a kasuwa.