Alaka Ta Kara Tsami: Nijar Ta Zargi Tinubu da Neman Kassara Ta

Kasar Nijar ta bayyana damuwa kan yadda Najeriya ke ci gaba da neman kawo tarnaki ga gwamnatin sojoji a Nijar. Ministan harkokin wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare, ya zargi Najeriya da hadin guiwa da wasu kasashe don kawo cikas ga mulkin sojin da ke jagorantar Nijar.

Bakary Yaou Sangare ya gayyaci jakadan Najeriya don tattaunawa kan wannan barazana. Ya bayyana cewa Najeriya na goyon bayan wasu ƙungiyoyi da ke neman kawo rashin zaman lafiya a Nijar, musamman bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a shekarar 2023.

Rikicin ya samo asali ne daga juyin mulki na shekarar 2023, wanda ya katse huldar Nijar da kungiyar ECOWAS. Ministan ya nuna bacin ransa kan kokarin da Najeriya ke yi na kawo barazana ga kasar, yana mai cewa, “Muna bakin cikin cewa Najeriya ba ta daina zama wata mafaka ga wadanda ke haddasa rikici a Nijar ba.”

Wannan zargi ya jawo hankalin duniya kan yadda alakar Najeriya da Nijar ke kara tabarbarewa, musamman a lokacin da ake fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Al’ummar Nijar na fatan samun karin goyon bayan duniya wajen yaki da barazanar rikici.