
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa (Kannywood) Aishatul Umairah ta yi magana kan alakar da ke tsakaninta da mawaki Dauda Kahutu Rarara. A wata hira da ta yi da Dokin Karfe TV, wadda jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, A’isha ta ce alakarta da Rarara bayyananniya ce, ba soyayya ba.
Kafofin sada zumunta sun sha daukar zafi kan alakar Aisha da Rarara, musamman ganin irin kusancin da ke tsakanin mutanen biyu. Jarumar ta bayyana cewa mutane na zargin soyayya tsakaninsu saboda irin shakuwar da ke tsakaninsu. “A baya na fada, komai muna yi shi tamkar mu ‘yan biyu ne. Yanzu ma zan sake maimaitawa, koda yaushe muna yin abu tare, shi ya sa ake ganin haka.”
Game da rade-radin cewa Rarara ya kai kudin sadakinta, Aishatul Umairah ta karyata hakan. Tana Mai cewa”karya ne ba a kai ba wallahi,” in ji ta. Ta kuma ce ba ta san ko akwai soyayya tsakaninsu ko babu.
A wani labarin kuma, jaruma Aishatul Umairah ta yi karin haske kan alakarta da babban furodusar masana’antar, Abubakar Bashir Maishadda. Humaira ta bayyana cewa sabanin abun da mutane ke tunani, babu wani abu da ya danganci soyayya tsakaninta da Maishadda illa kawai abokin sana’arta ne da suka shaku.