Addu’ar Samun Nutsuwa: Neman Kwanciyar Hankali da Natsuwa da tsari a gurin Allah

A yau, mun kawo muku addu’ar samun nutsuwa, wacce take cike da hikima da kuma ma’anoni masu zurfi. Wannan addu’a tana koyar da mu muhimmancin neman kwanciyan hankali daga Allah SWT, da kuma gode masa da ni’imomin da ya yi mana.

Addu’ar:

اللّهُـمَّ إِنِّي أَعْوذُ بِكَ مِنَ الهَـمِّ وَ الْحُـزْنِ والعًجْـزِ والكَسَلِ والبُخْـلِ والجُـبْنِ وضَلْـعِ الـدَّيْنِ وغَلَبَـةِ الرِّجال

“”Ya Allah, ina neman tsira a wurinka daga bakin ciki da damuwa, daga rauni da kasala, daga Rashin jin kai da tsoron fuskantar kalubale, daga cin bashi da kuma mika wuya ga mutane (wato wasu).”

Ma’ana:

Ma’anar wannan addu’a tana nuni da neman tsira daga wasu halaye marasa kyau da kuma kalubale na rayuwa.

Hikimar Addu’a:

Wannan addu’a tana da hikimomi da yawa, ciki har da:

  • Neman Kariya: Yin Addu’ar na bada kariya daga abubuwan da za su iya jawo damuwa ko rashin jin daɗi, wanda ke nuna bukatar taimakon Allah a cikin dukkan al’amuran rayuwa.
  • Neman Lafiya da Ƙarfi: Tana karfafa gwiwa ga mutum ya nemi lafiya da ƙarfi, yana tunatar da mu cewa rauni da kasala na iya shafar aiyyukan mu na yau da kullum.
  • Taimakon Allah: Ta hanyar neman tsira daga bashi da mummunan tasiri, mutum na nuna cewa yana dogara ga Allah SWT don samun kariya daga kalubale na rayuwa.
  • Kyakkyawan Halayya: Addu’ar na nuna muhimmancin kyawawan halaye kamar jin kai da juriya, wanda ke taimaka wa mutum ya zama mai amfani ga kansa da Kuma ga al’umma.

Yadda Ake Karanta Addu’ar:

Wannan addu’a za a iya karantawa a kowane lokaci, a Kuma ko Wani yanayi Ana iya karanta ta a fili ko a zuci.

Kammalawa:

Muna fatan wannan addu’ar samun nutsuwa da Kwanciyar hankali ta kasance mai amfani a gare ku. Muna kuma fatan Allah ya kwantar da hankalinmu, ya kuma ba mu nutsuwa. Ya kuma kare mu daga damuwa da tashin hankali. Ya tsare mu daga sharrin bashi da sharrin miyagun mutane Amin.

Wannan adduar tana cikin littafin Hisnul Muslim