Addu’ar Bude Kwakwalwa: Neman Ilimin kyawawan ayyuka   

A yau, muna kawo muku addu’ar bude kwakwalwa, wacce take cike da hikima da kuma ma’anoni masu zurfi. Wannan addu’a tana koyar da mu muhimmancin neman ilimin da kwadayin aikata kyawawan aiyukka

Addu’ar:


Ma’ana:
اللَّهُمَّ إنِّى أَسْألُكَ عِلْمَاً نَافِعاً وَ رِزْقاً طَيِباً وَ عَمَلاً مُتَقَبَلاً

“Ya Allah! Ina rokonKa da ka bani Ilimi mai amfani, kyakkyawar guzuri da ayyuka da za a karɓa


Wannan addu’a tana neman bude kwakwalwa, haskaka zuciya, karfafa tunani, saukaka fahimtar abubuwa, da kuma neman ayyukar ka ta zama karbabiya

Hikimar Addu’a:

Wannan addu’a tana da hikimomi da yawa, daga cikin su akwai:


Neman ilimin Sanin Allah: Ilimin Sanin Allahu SWT shine ne mafi girman ilmi, kuma wannan addu’a tana koyi da haka .
Neman hikima: Hikima tana taimaka mana mujen mu’amalan mu ta yau da kullum , kuma wannan addu’a tana koyi da hakan.
Ayyuka Masu Kyau: Tana karfafawa da mutum ya gudanar da ayyuka masu kyau, yanamai mai da hankali ga aikin da zai Allahu SWT zai karba, wanda ke nuni da cewa ayyuka suna da alaƙa da sakamakon da za a samu a lahira.
Neman karfafa tunani: Karfafa tunani yana taimaka mana wajen Mai da hankali da kuma tunawa da abubuwa.
Taimakon Allah: Addu’ar tana Kara jadadda dogaro ga Allah wajen neman dukkan abubuwan alkheri a rayuwa, yana nuna cewa mutum ba zai iya samun nasara ba idan ba tare da taimakon Allah ba.


Yadda Ake Karanta Addu’ar:

Wannan addu’a za a iya karantawa a kowane lokaci, amma ana fi son karanta ta da safe da maraice. Ana iya karanta ta a fili ko a zuci.

Kammalawa:

Muna fatan wannan addu’ar bude kwakwalwa ta kasance mai amfani a gare ku. Muna kuma fatan Allah ya bude mana kwakwalwa, ya kuma haskaka mana zuciya, ya kuma bamu arziki Mai Albarka, ya kuma tsarkake mana aiyyukan mu Amin.

Ana iya samun wannan adduar a cikin littafin Hisnul Muslim