
Addu’ar neman biyan bukata a wajen Allah tana da matukar muhimmanci a rayuwar Musulmi. Ga wasu daga cikin addu’o’in da za a iya amfani da su:
1. Addu’ar Annabi Ibrahim (A.S):
ربي اني لما انزلت الى من خير فقير
“Rabbi inni li ma anzalta ilayya min khayrin faqir.”
“Ya Ubangiji, ni a gare Ka ne na ke neman duk wani Alheri da Ka saukar mini, domin ni mai bukata ne.”
A cikin wannan addu’a, mai addu’a yana bayyana:
1. Neman Alheri:Yana rokon Allah da ya ba shi wasu alheraia ko taimako da ya saukar a duniya.
2. Bukatarsa: Yana tabbatar da cewa yana cikin bukata, wanda ke nuna tawali’u da sanin cewa yana bukatar taimakon Allah a rayuwarsa.
Wannan addu’a tana nuna imani da tawali’u, tare da neman taimako daga Allah a cikin al’amuransa.
2. Addu’a a lokacin bukata:
اللهم إني أسألك من فضلك ورحمتك، فإنك أنت الغفور الرحيم.
“Allahumma inni as’aluka min fadlika wa rahmatika, fa innaka anta al-Ghafur al-Rahim.”
Ya Allah, ina rokonka daga rahamarka da fadarka, kai ne mai gafara da jin kai
A cikin wannan addu’a, mai addu’a yana neman:
1. Rahama: Neman gata daga Allah, wanda ke nufin samun taimako da jin kai.
2. Falala: Neman alkhairi da kyautatawa daga Allah.
3. Gafara: Neman gafarar Allah daga zunubai da laifuka, yana mai tabbatar da cewa Allah mai juriya ne da jin kai.
Hikimomin wadanan addu’ar
Ga wasu daga cikin hikimomin :
1. Neman Rahama:
Addu’ar tana nuna cewa mai addu’a yana neman rahamar Allah, wanda ke nuni da bukatar taimako da jin kai daga gare Shi.
2. Neman Falala:
Ambaton “min fadlika” yana nufin neman kyaututtuka, wanda ke jaddada cewa Allah ne mai bayar da ni’imomi da alkhairi.
3. Gafara da Jin Kai:
Kalmar “al-Ghafur al-Rahim” tana tabbatar da cewa Allah mai gafara ne da jin kai, yana nuna cewa mai addu’a yana da tabbacin samun gafara da taimako.
4. Yarda da Allah mai bayarwa ne:
Addu’ar tana bayyana cewa duk wani alheri da bawa zai samu yana zuwa ne daga Allah, kuma babu wani abu da mutum zai iya samu ba tare da yardarSa ba.
5.Nuna tawali’u da karɓar ƙaddara: Mutum yana nuna tawali’unsa da sanin cewa ya dogara kacokan ga Allah a dukkan al’amuransa. Wannan yana nuna rashin girman kai ko alfahari.
6. Karfafa hakuri da dogaro: Addu’ar tana koya mana muhimmancin hakuri da kuma dogaro ga Allah yayin fuskantar wahalhalu ko matsaloli.
Yadda Ake yin adduar
Neman gafara: Kafin ka yi addu’a, yana da kyau a fara da neman gafarar Allah daga dukkanin zunubai.
Nuna godiya: A nuna godiya ga Allah kan dukkan ni’imomin sa.
Dawainiya: A yi addu’a da zuciya daya, A yi imani cewa Allah zai amsa.
A Yayin da Mai bukata yake Sallar Farilla ko Nafila se ya yawai ta anbaton wadan Nan adduo’i