
Jam’iyyar ADC ta musanta zargin da wani hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya yi na cewa jam’iyyun adawa na shirin kifar da gwamnatin Bola Tinubu kafin zaben 2027. Kakakin rikon kwarya na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar su ba ta da niyyar yin juyin mulki ko wata hanya da ta sabawa dimokuradiyya. Ya jaddada cewa suna ganin kuri’a a matsayin hanyar da za su yi fafatawa da jam’iyyar APC.
A cewarsa, “Mu ba sojoji ba ne, mu ‘yan siyasa ne. Ba mu da alburusai sai kuri’u.” Ya kara da cewa, idan lokacin ya yi, za su gabatar da manufofinsu ga al’umma, sannan su bar ‘yan kasa su yanke hukunci.
Bolaji ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakatar da hadimansa daga yada zarge-zargen da ka iya haddasa hargitsi a kasa, yana mai cewa ana bukatar a daina yada irin wannan zargin da zai iya tada tarzoma, musamman a wannan lokaci da zabe ke karatowa.
Wannan martani na ADC na zuwa ne bayan zargin da aka yi, wanda ya jawo cece-kuce a fagen siyasa, musamman a tsakanin jam’iyyun adawa. Jam’iyyar ADC ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su ki yarda da duk wani yunkuri da zai hana adawa fadin albarkacin bakinsu ko hana su shiga fafatawa a siyasa.