Abin da Ya Sa Gwamnonin Najeriya Suka Bukaci Tinubu Ya Janye Kudirin Haraji

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana dalilin da ya sa gwamnonin jihohin Najeriya suka nemi a janye kudirin sauya fasalin haraji da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar. A cewarsa, gwamnoni suna son samun karin lokaci domin tattaunawa kan kudirin kafin a miƙa shi ga majalisa.

Gwamna Sule ya bayyana cewa ba dukkan gwamnonin jihohi 36 ke adawa da kudirin ba, illa suna bukatar a tattauna da juna da kyau kafin a yanke shawara. Ya yi bayanin cewa akwai wasu matsaloli da aka tsallake, wanda hakan ya sa gwamnonin ke damuwa. Ya ce, “Matsalolin da aka tsallake sun fi damun mu game da wannan sabon kudiri.”

Sule ya jaddada cewa akwai wasu kulle-ƙulle da ke bukatar a warware su, kamar batun ƙara kason da ake warewa. Ya yi nuni da cewa, “Idan aka ɗaga kason VAT daga kashi 20 zuwa 60, wannan ba zai yi wa jihohi da dama kyau ba.” Ya nuna cewa akwai bukatar a zauna a tattauna wa da juna kafin a yanke hukunci.

A cikin wannan yanayi, gwamnan ya ce ya kamata a gudanar da tattaunawa kafin a miƙa kudirin ga majalisa. Ya bayyana cewa, “Wannan taron da Channels TV ta shirya ya kamata ya kasance tun kafin a miƙa kudirin ga majalisa.” A cewarsa, wannan rashin cikakken bayani kan kudirin yana daga cikin manyan damuwar gwamnonin Najeriya.

Gwamna Sule da sauran gwamnonin suna fatan a janye kudirin haraji na Tinubu don a sake tattauna wa da juna da kuma fahimtar dukkanin abubuwan da ke ciki. Wannan yana nuna cewa akwai bukatar jin ra’ayin gwamnonin jihohi kafin a yanke hukunci kan kudirin haraji wanda zai shafi tattalin arzikin ƙasar gaba ɗaya.