
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Damboa/Gwoza/Chibok, Hon. Ahmadu Jaha, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya janye kudurin gyaran haraji daga majalisar tarayya. Ya bayyana cewa ‘yan Najeriya za su amince da kudurin ne kawai idan an yi gyara a sassan da aka nuna adawa dasu.
A yayin wata hira da NTA News, Jaha ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi wa kudurin gyara, yana mai cewa:
“Abin da muke ba gwamnati shawara shi ne, ta janye wannan kudiri daga majalisar tarayya, a yi kwaskwarima a bangarorin da aka fahimci ana adawa da su.”
Ya kuma jaddada cewa idan Tinubu yana son taimakawa jihohin Najeriya, ya kamata ya rika raba kaso 20% na harajin kamfanoni ga inda ake amfani da kayayyakinsu.
Jaha ya nuna damuwa game da yadda shugaban kasa ya ki yin la’akari da kiran janye gyaran harajin a lokutan da ake ta neman hakan. Ya tuno da kalaman tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, yana mai cewa, “Arewa ba malalata ba ne.” Ya bayyana cewa al’ummar Arewa suna da manyan mutane kamar Aliko Dangote da Abdulsamad Isyaku Rabiu, wanda hakan ke nuna cewa suna da karfin gwiwa.
Hon. Jaha ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saurari ra’ayoyin al’umma, musamman ma a lokacin da ake fuskantar sabbin canje-canje a tsarin haraji. Wannan yana nuni da cewa akwai bukatar a yi la’akari da ra’ayin jama’a kafin a yanke hukunci kan kudurin gyaran haraji wanda zai shafi dukkan jihohi.