
Lauya Abba Hikima ya sanar da janye shirin tafiyarsu zuwa jihar Edo bayan gwamnatin Kano ta kafa kwamiti don binciken kisan da aka yi wa ‘yan Arewa a jihar. Wannan mataki ya biyo bayan sabbin rahotanni da suka nuna cewa gwamnatin jihar ta yi alkawarin tabbatar da hakkin mutanen da aka kasha.
A cikin sanarwa da ya fitar, Hikima ya bayyana cewa suna da tabbacin cewa kwamiti da aka kafa zai gudanar da bincike mai zurfi kuma zai fitar da cikakken rahoto kan lamarin. Ya ce, “Muna son ganin cewa an kamo wadanda suka aikata laifin da kuma hukunta su cikin gaggawa.”
Hikima da abokansa sun bayyana cewa sun yanke shawarar fasa tafiya domin ba wa kwamitin damar gudanar da aikin da ya dace. Sun jaddada cewa suna fatan za a samar da tsaro a kudancin Najeriya, tare da kafa kotu ta musamman domin hukunta wadanda aka zargi da aikata kisan.
Gwamnatin Kano ta kafa wannan kwamiti ne a makon jiya, tare da alkawarin cewa za a karɓi duk wani rahoto da zai taimaka wajen tabbatar da adalci ga wadanda aka kashe. Lauyan ya bayyana cewa suna sa ran samun kyakkyawan sakamako daga wannan kwamiti.
Haka zalika, sun bukaci a samar da dokoki masu tsauri don hana maimaituwar irin wannan ta’asa a nan gaba. Wannan mataki ya zo a lokacin da ake fuskantar tashe-tashen hankula a jihar Edo, wanda hakan ya jawo hankalin hukumomi da dama.