
Tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya ta fara horar da maza, musamman wadanda ke shirin aure. Yanzu maza suna raba kafa a soyayya, suna neman mata da ba za su yi masu tsada sosai ba a lokacin aurensu.
An gano cewa maza da yawa yanzu suna soyayya da ‘yan mata da dama, kuma suna tambayar matan su basu kiyasin kudin da za su kashe a lokacin aurensu. Wannan yana taimaka musu su yanke shawara ko za su auri matar ko kuma su nemi wata.
Ayi tattaunawa da wasu samari da ‘yan mata kan irin dabarar da mazan ke amfani da ita wajen neman aure a yanzu. Wasu samari sun ce suna tambayar matan su basu jerin abubuwan da suke bukata na aurensu, ciki har da kayan lefe, sadaki, da kudin biki. Wasu kuma suna tambayar matan su basu kiyasin kudin da za su kashe a biki, domin su san ko za su iya biyan kudin.
Wani saurayi da aka tattauna dashi ya ce: “Yanzu dole ne mu yi taka tsantsan wajen neman aure, domin tsadar rayuwa ta yi yawa. Muna tambayar matan mu basu jerin abubuwan da suke bukata na aurensu, domin mu san ko za mu iya biyan kudin.”
Wata yarinya ma ta ce: “Ba na son wannan sabon salon da mazan ke amfani da shi wajen neman aure. Ina ganin cewa soyayya ba game da kudi ba ne. Dole ne mazan su yi soyayya da mu domin halayenmu da kuma mu’amalan mu, ba domin kudin da za su kashe a lokacin aurensu ba.”
Wasu masana sun ce wannan sabon salon da mazan ke amfani da shi wajen neman aure na iya haifar da matsaloli a nan gaba. Suna ganin cewa zai iya sa mazan su auri matan da ba sa so sosai, kawai domin su yi auren da ba zai yi masu tsada sosai ba.
A karshe, dole ne maza da mata su yi taka tsantsan wajen neman aure.Dole ne su yi soyayya da juna domin Kara Sanin halayen juna, ba domin kudin da za su kashe a lokacin aurensu ba.