
Ana zargin akwai baraka a jam’iyyar APC da ke jihar Jigawa tsakanin tsohon gwamnan jihar, Badaru Abubakar da Gwamna Umar Namadi.
Wani rahoton Vanguard ya ce lamarin ya faro ne tun lokacin kaddamar da yan Majalisa a jihar da zaben kakakinta a watan Yunin 2023.
Yayin wata ganawa, an amince za a zabi Idris Garba kakakin Majalisar wanda daga bisani gwamnan ya sauya ra’ayi inda ya goyi bayan Haruna Dangyatin wanda bai yiwa masoyan Badaru dadi ba.
Daga bisani an yi kokarin tsige kakakin Majalisar wanda ya sha da kyar, a kokarin daukar fansa a wancan lokaci inda Dangyatin ya dakatar da wasu ciyamomi da ake ganin yaran Badaru ne kan zargin badakala.
Bayan fashewar tankar mai da ta yi ajalin mutane da dama a karamar hukumar Taura, Badaru ya tura tawaga inda ya ba da gudunmawar N20m ba tare da kula gwamnatin jihar ba kamar yadda wasu suka yi.
Hakan ya batawa na kusa da gwamnan rai da suke ganin Badaru na kokarin kaskantar da mai gidansu, cewar Premium Times.
Wata kungiyar APC Vanguard ta zargi Badaru da mu’amala da wasu yan adawa inda ta ce hakan babbar barazana ce ga jam’iyyar a kowane mataki.
Shugaban Kungiyar, Salisu Yakubu ya bukaci Bola Tinubu ya taka masa birki ka da abin da ya faru da Goodluck Jonathan a 2015 ya maimaita kansa.
Gwamna Namadi ya magana kan zargin matsala a APC bayan dawowa daga hutun makwanni uku inda ya ce babu matsala a jam’iyyar.
Ya tabbatar da cewa bayan ba shi nan abubuwa da dama sun faru inda ya koka kan yadda wasu ke kokarin kawo rigima tsakanin yan jam’iyyar.