
Gwamnonin jam’iyyar PDP sun shiga ganawa ta musamman a jihar Plateau domin tattauna matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta da kuma jero tsare-tsaren kawo sauyi a kasar nan.
Mai masaukin baki, Gwamna Caleb Mutfwang ya tabbatar da himmatuwarsu wurin kawo hadin kai a jam’iyyar, cewar Leadership.
Ya kuma ba da tabbacin dawo da martabar jam’iyyar a idon yan Najeriya kamar yadda take.
Gwamna Mutfwang ya godewa gwamnonin PDP da kuma masu ruwa da tsakin jam’iyyar da suka cika a jihar domin wannan taro.
Duk da wannan taro musamman an shirya ne domin gwamnoni, amma abin farin ciki ne yadda jiga-jigan jam’iyyar suka cika wannan taro domin ba gwamnonin goyon baya.”
Jam’iyyar PDP ba iya zakulo hanyoyin kawo zaman lafiya a cikinta za ta yi ba har da dawo da martabar jam’iyyar a idon yan Najeriya.”
Caleb Mutfwang
Daga bisani, Gwamna Mutfwang ya bayyana tasirin jihar Plateau a bunkasa jam’iyyar tun farkon kafa ta.
Ya kuma ba da tabbacin dawo da martabar jam’iyyar a idon yan Najeriya.
Gwamna Mutfwang ya godewa gwamnonin PDP da kuma masu ruwa da tsakin jam’iyyar da suka cika a jihar domin wannan taro.