NiMet Ta Yi Hasashen Ruwan Sama a Kano da Sauran Jihohi

Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar da cewa za a samu ruwan sama mai ƙarfi a sassan Arewa da Kudancin Najeriya a ranar Juma’a, 25 ga Yuli, 2025. Hasashen ya shafi jihohin kamar Kano, Katsina, Bauchi, da Borno, inda aka sa ran za a fuskanci tsawa da ruwan sama.

A cikin sanarwar da NiMet ta fitar, an bayyana cewa daga safiyar ranar Juma’a, akwai yiwuwar haduwar hadari da yayyafi a Arewacin Najeriya, musamman a jihohin Jigawa, Gombe, Kaduna, da Adamawa. Daga yammaci zuwa dare, ruwan sama mai karfi zai sauka a jihohin Taraba, Sokoto, da Yobe.

NiMet ta shawarci jama’a da su yi taka tsantsan, musamman a yayin tuki, domin kaucewa haɗurra da kuma guje wa fadowar reshen bishiyoyi yayin guguwa. Hakanan, hukumar ta bukaci kamfanonin jiragen sama da su duba rahoton yanayin filin jirgin kafin tsara zirga-zirgarsu.

Shawarar NiMet ga al’umma ta haɗa da tunatar da mutane kan yiwuwar ambaliyar ruwa da iska mai ƙarfi, wanda zai iya shafar al’amuran yau da kullun. Jama’a na da bukatar su kasance masu lura da sabbin bayanai daga shafin hukumar domin kiyaye lafiyarsu da dukiyoyinsu.