
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ziyarar ta’aziyya da ya kai jihar domin jajanta wa al’ummar jihar da iyalan marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata. Wannan ziyara ta kasance a lokacin da ake cikin jimamin rasuwar fitaccen ɗan kasuwa.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafin Facebook, Gwamna Abba ya ce ziyarar Tinubu na nuni da jagoranci na gaskiya da tausayi. Ya bayyana cewa wannan ziyara ta kawo karin kwanciyar hankali ga al’ummar Kano a wannan lokaci mai wuya.
Gwamna Abba ya yaba da matakan da shugaban ƙasa ya ɗauka, ciki har da tura tawagar jami’an gwamnatin tarayya zuwa wajen jana’izar a Madina, Saudiyya. Ya ce wannan goyon baya ya taimaka wajen gudanar da jana’izar cikin mutunci da ƙima.
Haka zalika, Alhaji Tajudeen Aminu Dantata, babban ɗan marigayin, ya bayyana godiyarsa ga Tinubu bisa goyon bayan da ya bayar a lokacin da mahaifin su ke raye da kuma bayan rasuwarsa. Ya tabbatar da cewa za su ci gaba da girmama kyawawan halayen da mahaifinsu ya bar musu.
Shugaba Tinubu ya bayyana marigayi Dantata a matsayin mutum mai gaskiya da tawali’u, yana mai rokon Allah ya sanya shi a Aljannah Firdaus. Wannan ziyara ta jawo hankalin al’umma, tare da nuna hadin kai da alakar da ke tsakanin gwamnati da al’ummar jihar Kano.