
Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhu barkan mu da war haka, Ina muku maraba da ziyartan wanan blog dinmu, yau mauduin Zai kasance akan Addu’ar kariya Daga makiya
A rayuwar mu ta yau da kullum, mu kasance masu fuskantar kalubale da dama, ciki har da barazanar makiya. Makiya na iya zama daga cikin mutane ko kuma mugayen abubuwan dazadu iya shafar lafiyarmu, dukiya, da zamantakewar mu. Saboda haka, addu’a na da matukar muhimmanci wajen samun kariya daga irin wannan barazana.
Mece Ce Addu’a?
Addu’a ita ce hanyar da Dan Adam ke ni Dan ya sadu da Ubangiji Allahu SWT, inda muna neman taimako, kariya, da tsari daga gare Shi. A cikin Al-Qur’ani Mai girma da Hadisin Sunnah, an karfafa yin addu’a a duk lokacin da muke fuskantar Wata wahala ko barazana. Addu’a na iya zama ga mutum daya ko kuma ga al’umma baki ɗaya. Bugu da kari musulunci ya koyar wa Iyaye da su kasance masu yiwa Yaran su Addu’ar a Koda yaushe, Cikin harda Addu’ar kariya Daga makiya
Addu’ar Kariya Daga Makiya
Akwai addu’o’in da aka tabbatar suna bayar da kariya daga makiya. Daga cikin Alqur’ani Mai girma akwai addu’oi kamar haka
رَبِّ نَجِّنِي مِنَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ
Rabbi najjinee mina alqawmi alththalimeen
Ubangijina! Ka tsĩrar da ni daga mutãne azzãlumai
رَبِّ انْصُرْنِي عَلَى الْقَوْمِ الْمُفْسِدِينَ
Rabbin surnee alal qawmil mufsideen
Ubangijina! Ka taimake ni a kan mutãne bata gari
An samu Hadisin Wanda “Ibn ‘Abbaas (Allah ya Kara masa yarda) ya ruwaito cewa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana yawan mika Hassan da Hussain ga kariyar Allah yana mai cewa:”
أُعيـذُكُمـا بِكَلِـماتِ اللهِ التّـامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْـطانٍ وَهـامَّة، وَمِنْ كُـلِّ عَـيْنٍ لامَّـة
’U’eedhukumaa bikalimaatil-laahit-taammati min kulli shaytaanin wa haammatin, wa min kulli ‘aynin laammatin.
Ina neman tsari gare ku da kalmomin Allah cikakku daga kowane shaidani da kowane mugun dabba da kowane ido mai hassada.
Kamar yadda misali yazo a Cikin wannan Hadisin, Manzo SAW ya kasance Yana karanta wannan Addu’ar wa jikokin sa Hassan da Hussain domin Kare su Daga sharrin makiya, Ana yin wannan Addu’ar ma Yara domin Kare su da sharrin makiya
Kafin ayi Addu’ar, ku kasance Kuna wasu imanin cewa Allah ne Mai karewa, Kuma shine Ubangiji gagara misali, shine Mai biyan dukkan bukata Kuma shine Mai Jarabtan ko Wani bawan sa, yadda yaso, a ko wani lokacin da yaga dama
Kammalawa
Addu’a na da matukar muhimmanci a rayuwarmu, musamman wajen samun kariya daga makiya. A cikin dukkan halin da muke ciki, kada mu manta da yin addu’a, domin wannan hanya ce ta samun taimako daga Allah. Allah ya sa mu kasance cikin kariya, kuma ya gafarta mana dukkan kurakuramu. Allah Kuma yasa mu dace Ameen.
Godiya gareku mungo de sarai