
Addu’ar Kariya Daga Sihiri a Cikin Tsarin Musulunci
A addinin Musulunci, addu’a tana da matukar hanfani da muhimmanci. Ta hanyar yawan anbaton addu’a, Musulmai suna neman kariya daga dukkanin sharrin dake cikin duniya, ciki har da sihiri, wanda yake daga cikin abubuwan da ke jawo damuwa ga mutane. Sihiri na iya zama abu mai hatsari wacce ke iya shafar rayuwar mutum da lafiyarsa, don haka yana da kyau muyi amfani da addu’o’in da musulunci ya koyar da mu.
Ita Sihiri Mecece?
Sihiri a cikin addinin Musulunci yana nufin amfani da wasu hanyoyi ko kuma amfani da wasu kayayyaki da ba su dace ba, don cimma burin Wani abu da Allah bai yarda da shi ba Kuma ya saba wa umarnin Sa.
Alkur’ani na bayyana cewa sihiri yana daga cikin sharrin shaidanu, wanda ke kawo cikas ga al’umma. Ubangiji Allahu SWT gargaɗi a cikin Alkur’ani, musamman a cikin surar Falaq da Nas.
Amfanin Addu’a don Kariya Daga Sihiri
Addu’a tana da matukar tasiri wajen kare Wanda yayi shi daga sharrin sihiri. Akwai wasu addu’o’in da aka saba amfani da su don neman kariya daga Sihiri:
1. Ayat al-Kursi
Ayat al-Kursi, wanda yake cikin sura ta 2, aya ta 255, yana da karfi wajen kare mutum daga sharrin duniya. Ana karanta wannan aya bayan ko Wani sallan farilla da kuma kafin barci.
اللهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ
Allaahu laa ‘ilaaha ‘illaa Huwal-Hayyul-Qayyoom, laa ta’khuthuhu sinatun wa laa nawm, lahu maa fis-samaawaati wa maa fil-‘ardh, man thai-lathee yashfa’u ‘indahu ‘illaa bi’ithnih, ya’lamu maa bayna ‘aydeehim wa maa khalfahum, wa laa yuheetoona bishay’im-min ‘ilmihi ‘illaa bimaa shaa’a, wasi’a kursiyyuhus samaawaati wal’ardh, wa laa ya’ooduhu hifdhuhumaa, wa Huwal- ‘Aliyyul- ‘Adheem.
Allah! Babu abin bautawa bisa cancanta sai Shi, Rayayye, Mai rayawa, kuma Ya tsare dukkan abin da yake akwai. Barci ko gyangadi ba ya riske shi. Shi ne da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. Wane ne wanda ke yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Ya san abin da zai same su a duniya, da abin da zai same su a Lahira. Kuma bã zã su kẽwayãwa da kõme ba daga ilminSa, fãce abin da Ya so. Al’arshinSa ya shimfiɗa sammai da ƙasa, kuma bã Ya jin gajiyar tsare su da tsare su. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma
2. Suratul Falaq da Suratul Nas
Wannan surorin guda biyu suna da matukar tasiri wajen neman kariya daga sharrin masu sihiri da shaidanu. Ana karanta su tare da niyyar samun kariya daga dukkanin Sahiri
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلْفَلَقِ, مِن شَرِّ مَا خَلَقَ, وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ, وَمِن شَرِّ ٱلنَّفَّـٰثَـٰتِ فِى ٱلْعُقَدِ, وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai
Ka ce: Ina nẽman tsari ga Ubangijin safiya
Daga sharrin abin da Ya halitta
Kuma daga sharrin dare idan yayi duhu
Kuma daga sharrin masu yin busa a kan ƙulle-ƙulle
Kuma daga sharrin mai hasada idan ya yi hasada.”
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ, قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاس, ِمَلِكِ ٱلنَّاسِ, إِلَٰهِ ٱلنَّاس, ِمِن شَرِّ ٱلْوَسْوَاسِ ٱلْخَنَّاس, ِٱلَّذِى يُوَسْوِسُ فِى صُدُورِ ٱلنَّاسِ, مِنَ ٱلْجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ
Bismillahir-Rahmanir-Raheem
Qul a’udhu birabbin-naas
Malikin-naas
Ilahin-naas
Min sharril-waswasil-khannaas
Allazhi yuwaswisu fi sudoorin-naas
Minal jinnati wan-naas
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai.
Ka ce: “Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne
Mammalakin mutane
Abun bautan mutane
Daga sharrin mai waswasi mai ja da baya
Wanda ke sanya waswasi a cikin zukatan mutane.
Daga aljannu da mutane.
3. Addu’ar Hasbiya llahu: A Cikin Sunna, an koyar da a dinga yin wannan Addu’ar so bakwai (7) da Safe a yayin azkarul Sabahi da Kuma so bakwai (7) da maraice a ayayin azkarul Masahi
حَسْبِيَ اللهُ لَآ إِلَهَ إِلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ
Hasbiyallaahu laa ‘ilaaha ‘illaa Huwa ‘alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-‘Arshil-‘Adheem
Allah shine ma’ishina, babu abin bautawa da gaskiya sai shi, a gare shi nake dogara, kuma shi ne Ubangijin Al’arshi maɗaukaki.
Yadda Muslim zaiyi Addu’ar
1. Neman Natsuwa da Tsoron Allah: Kafin ka fara addu’a, ka kasance akwai natsuwa a cikin zuciyarka. Ka kasance da tsoron Allah, domin Allah yana tare da masu imani.
2. Karanta Addu’ar da Imani: Yi imani da addu’ar da kake karantawa. Ka karanta ta kana Mai yakinin cewa Allah Ubangiji SWT Zai baka kariya, Kuma shine Mai Bada kariya
Kammalawa
A karshe, ya kamata mu gane cewa addu’a tana da matukar tasiri wajen kare kanmu daga dukkanin sharrin, ciki har da sihiri. Muna bukatar mu kasance masu tawakkali a ko Wani hali muka tsinci kanmu, mu kuma yi amfani da addu’o’in da musulunci ya koyar a kowane lokaci. Kada mu manta cewa Allah yana tare da masu imani, kuma yana da iko akan komai. Ta hanyar addu’a, zamu iya samun kariya daga dukkanin sharrin duniya da kuma samun zaman lafiya a rayuwar mu.