
Shugabannin kasashen Chadi, Gambiya, da Guinea Bissau sun tashi zuwa Daura, jihar Katsina, domin halartar jana’izar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. Gwamna Dikko Umaru Radda na Katsina ya bayyana wannan a wani taron manema labarai.
A cikin wannan taron, Radda ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tarbi gawar Buhari a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua kafin a wuce da ita zuwa Daura. Haka kuma, ministoci 25 daga gwamnatin tarayya za su kasance a Daura domin karɓar gaisuwar ta’aziyya a madadin gwamnatin Najeriya.
Gwamnan ya ce wannan mataki yana nuna mutuncin da Buhari ya samu a idon kasashen duniya. Ana sa ran jana’izar za ta gudana a gidansa a Daura da misalin ƙarfe 2:00 na rana, bayan isowar gawarsa daga London, inda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya tashi domin dauko gawar.
Wannan jana’iza ta zama mai tarihi, tare da jan hankalin masoya Buhari daga sassa daban-daban na Najeriya, wanda hakan ya sa gwamnati ta ayyana hutu a ranar Talata.