
Zainab Buba Galadima ta bayyana cewa sunan mahaifinta, Buba Galadima, yana kawo cikas ga samun alfarma a gwamnatin Bola Tinubu. A cikin wata hira da ta yi, Zainab ta bayyana cewa tun lokacin da Tinubu ya hau mulki, ba ta taba samun wata dama a gwamnati ba, kuma ba ta nemi kwangila ko wata aiki.
Zainab ta ce mahaifinta bai taba neman alfarma a gare su ba, wanda hakan ya jawo musu takura. Ta bayyana cewa a lokacin mulkin Muhammadu Buhari, ta yi aiki ba tare da an biya ta ba, kuma an hana ta samun wasu damarmaki saboda suna ganin mahaifinta na sukar gwamnatin.
Ta ce, “Aiki ma da nake a wurin ba albashi nake dauka ba, suna gani na babu yadda za su yi da ni suna tsoron korata a yi magana.” Zainab ta yi bayanin cewa, duk lokacin da ta nemi taimako, ana fada mata cewa ba za a iya taimaka mata ba saboda mahaifinta yana sukar gwamnati.
Haka zalika, Zainab ta yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta duba wannan hali, tana mai cewa akwai bukatar a yi adalci ga dukkan ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da asalinsu ba. Wannan jawabi na Zainab ya jawo hankalin al’umma, inda ake tattaunawa kan yadda sunan iyali ke shafar damar mutum a harkokin siyasa da gwamnatin Najeriya.