
Rundunar ƴan sandan Kano ta kaddamar da wani sabon shiri mai suna “Operation Kukan Kura,” wanda ya kai ga cafke mutum 98 da ake zargin da laifuka daban-daban. Kwamishinan ƴan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai.
CP Bakori ya bayyana cewa an kirkiro wannan shiri ne domin inganta tsaro a jihar, tare da hana laifuffukan da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi. Ya ce an samu gagarumin ci gaba tun lokacin da aka fara gudanar da aikinta daga ranar 1 ga Yuli.
A cikin wannan lokaci, rundunar ta samu nasarori masu yawa, ciki har da kwato manyan makamai da motoci na sata, da kuma wasu kayan haram. Abubuwan da aka kwato sun haɗa da motoci shida, keke-napep takwas, da kuma miyagun kwayoyi da dama, wanda hakan ke nuna yadda rundunar ta yi nasara wajen dakile laifuka a jihar.
CP Bakori ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da goyon baya ga rundunar ƴan sanda, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen inganta tsaro da dawo da zaman lafiya a Kano. Wannan sabon shiri na “Operation Kukan Kura” na nufin tabbatar da cewa mutane suna zaune cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ba.