Oyedepo Ga Mambobin Cocinsa: “Kada Ku Sake Zaben Wauta a 2027”

Babban malamin addinin Kirista, Bishop David Oyedepo, ya yi kira ga mambobin cocin Living Faith Church, da aka fi sani da Winners Chapel, da su yi amfani da hankali da basira wajen zaben 2027.

A yayin wani wa’azi da ya gabatar, Oyedepo ya tambayi wadanda suka sayar da kuri’unsu a zaben da ya gabata ko kudin da aka ba su har yanzu yana nan. Ya kuma yi Allah wadai da lalacewar tsarin raba mukamai a kasar.

“Kudin da aka ba ku a zaben da ya gabata, ina da tabbacin har yanzu yana nan. Ban tsammanin wani memba na wannan coci zai sake yin wauta a wannan karon ba. Yau ana yayata tikitin Musulmi da Musulmi, gobe kuma za a yayata Fulani da Fulani, jibi kuma gwamnoni za su mika wa ‘yan uwansu, saboda an riga an lalata tsarin raba mukamai….” in ji Oyedepo.

Kalaman Oyedepo sun jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke goyon bayansa, wasu kuma ke sukar sa. Wasu daga cikin wadanda suka mayar da martani sun bayyana damuwarsu game da halin da kasar ke ciki, suna masu cewa tribalism ya yi wa kasar illa.

Wasu kuma sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da hankali da basira wajen zaben 2027, su zabi shugabannin da za su kawo ci gaba a kasar.