APC Na Neman Jan Gwamnoni Biyar Zuwa Jam’iyyarta

Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa tana ƙoƙarin jawo gwamnoni biyar zuwa cikin jam’iyyarta, a daidai lokacin da wasu manyan ‘yan siyasa da ‘yan majalisa ke sauya sheƙa zuwa APC, tare da mara wa shugaba Bola Tinubu baya domin sake tsayawa takara a 2025.

Wannan bayani ya fito ne a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Punch ta yi da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a shiyyar Kudu maso Gabas, Dr. Ijeoma Arodiogbu.

A cewar Arodiogbu, gwamnonin da ake sa ran zasu sauya sheƙa sun hada da na jihohin Bayelsa, Ribas, Filato, Kano, da kuma Abia ko Enugu. Ya ce, “A cikin watanni biyu masu zuwa, za ku ga sun shigo jam’iyyar a hukumance.”

Wannan ci gaba na zuwa ne bayan da gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya sauya sheƙa zuwa APC tare da ‘yan majalisa da kuma dukkan shugabannin jam’iyyar PDP a jihar.

Hakazalika, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon gwamna kuma mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a 2023, Ifeanyi Okowa, da kuma wasu ‘yan majalisa, sun shiga jam’iyyar APC a watan Afrilu.

Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, na jam’iyyar APGA, shi ma ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a karo na biyu, yayin da ake ta rade-radin cewa wasu manyan ‘yan siyasa a jam’iyyar NNPP, ciki har da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, da gwamna Abba Yusuf, da gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, na iya mara wa shugaban ƙasa baya a 2027.

Arodiogbu ya yi watsi da ƙoƙarin haɗin gwiwar ‘yan adawa, yana mai cewa “Wannan batun ƙirƙirar wani haɗin gwiwar ‘yan adawa ba komai ba ne face wani abin tallatawa a kafofin watsa labarai.”

Ya ce, “Waɗannan ‘yan siyasar kawai suna son su ci gaba da kasancewa a cikin labarai. Amma ‘yan Najeriya suna tare da jam’iyyar da ke kawo cigaba – wato APC.”