Azumi da Addu’a Domin Nema Mafita Kan Karancin Abinci a Najeriya

Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya ta ayyana kwanaki uku na azumi da addu’a domin neman taimakon Allah kan ƙalubalen karancin abinci da ake fama da shi a ƙasar.  Wannan sanarwar ta fito ne daga ofishin Daraktan Kula da Ma’aikata, Adedayo Modupe, a ranar 11 ga watan Yuni.

An ƙarfafa ma’aikatan ma’aikatar baki ɗaya da su shiga wannan azumi da addu’a, wanda za a gudanar a babban ɗakin taro na hedikwatar ma’aikatar da ke Area 11, Garki, Abuja, daga ƙarfe 12:00 na rana zuwa 12:30 na rana.

Za a fara azumin ne a ranar Litinin, 16 ga watan Yuni, sannan a ci gaba a ranakun 23 da 30 ga watan Yuni.  Taken zaman addu’ar shi ne “Shiga cikin addu’a domin kare ƙasa da neman cigaba.”

A cewar sanarwar, an shirya wannan addu’a ne domin neman shiriyar Allah da taimakonsa a ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi na magance matsalar karancin abinci a Najeriya.  Ƙasar na fama da matsin tattalin arziki da karancin abinci sakamakon abubuwa daban-daban, ciki har da sauyin yanayi, rashin tsaro, da hauhawar farashin kayayyaki.

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirye-shirye da dama domin inganta noman cikin gida da rage dogaro da abinci daga ƙasashen waje.  Duk da haka, farashin kayan masarufi kamar shinkafa, masara, da gero na ci gaba da zama barazana ga rayuwar al’umma, musamman talakawa.  Wannan ya sa ma’aikatar ta ga ya dace a nemi taimakon Allah ta hanyar azumi da addu’a domin samun mafita kan wannan matsala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *