Sojoji Sun Yi Nasara: An Kashe ‘Yan Ta’adda 60 a Jihar Borno

Sojojin Najeriya a karkashin Operation Hadin Kai sun kai wani gagarumin farmaki a garin Bita, jihar Borno, inda suka kashe aƙalla ‘yan ta’adda 60. Wannan farmaki ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lokacin da ‘yan ta’addan suka kai hari kan sansanin sojoji.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa sojojin sun yi amfani da jiragen yaki, ciki har da A-29 Super Tucano, wajen ragargazar mayakan Boko Haram. Wannan ya jawo mummunan hasara ga ‘yan ta’addan, tare da lalata motocin su guda biyu da ke dauke da bindigogi.

Bayan artabu mai tsanani da ya ɗauki kusan sa’o’i biyu da rabi, rahotanni sun tabbatar da cewa wannan farmaki na daga cikin mafi girma da sojojin Najeriya suka taba gudanarwa a kan Boko Haram a ‘yan kwanakin nan. Jami’an tsaro sun ci gaba da bibiyar ragowar ‘yan ta’addan da suka tsere, suna tabbatar da cewa nasarorin za su taimaka wajen rage karfin Boko Haram a yankin.

Ana sa ran wannan nasara za ta kara tabbatar da zaman lafiya a Arewa maso Gabas, yayin da sojoji ke ci gaba da fafutukar murkushe dukkanin kungiyar ‘yan ta’adda a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *