
Cibiyar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kaso 23.71 cikin 100 a watan Afrilu na 2025. Wannan rahoto ya nuna cewa an samu raguwar kashi 0.52 idan aka kwatanta da watan Maris.
Hauhawar farashin abinci ya ragu sosai, inda ya tsaya a kashi 21.26% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. A cikin watan Afrilu, an sami raguwar farashin abinci har zuwa kashi 2.06, wanda ke nuna cewa farashin kayan abinci yana dawowa cikin yanayi mai kyau.
NBS ta ce wannan sauki a hauhawar farashi na nuni da nasarar yunkurin gwamnatin Najeriya na dakile tashin farashi. Daga cikin kayayyakin abinci da suka ragu farashi sun hada da fulawa, masara, da shinkafa.
Jama’a na sa ran wannan yanayi zai ci gaba, musamman tare da matakan da gwamnati ta dauka don inganta tattalin arziki da rage wahalhalu ga talakawa.