Rikicin Cikin Gida Ya Sa ‘Yan Majalisar NNPP Biyu Sun Koma APC

‘Yan majalisar wakilai guda biyu daga jihar Kano sun fice daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Kabiru Usman da Abdullahi Sani, wadanda suke wakiltar mazabu na Rano/Bunkure/Kibiya da Karaye/Rogo, sun bayyana sauya shekar su a gaban kakakin majalisar.

Sauya shekar na zuwa ne a lokacin da jam’iyyar NNPP ke fuskantar rikice-rikice na cikin gida, wanda hakan ya jawo hankalin wasu fitattun ‘yan jam’iyyar da suka koma APC, ciki har da Sanata Kawu Sumaila.

Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ya karanta wasikun sauya shekar a gaban ‘yan majalisa, inda ya bayyana cewa wannan lamari na tabbatar da karuwar APC a fadin kasar. Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci zaman majalisar domin maraba da sababbin ‘yan majalisar.

A yayin da sauya shekar ya faru, Kwankwaso, jagoran NNPP, ya yi gargadi ga duk masu shirin fita daga jam’iyyar, yana mai cewa wannan mataki na cin amanar jam’iyya ne. Duk da haka, NNPP na ci gaba da fuskantar kalubale a Kano, inda wasu jiga-jigan jam’iyyar ke ficewa.

Ana sa ran wannan sauya shekar zai kara dagula al’amura a cikin NNPP, wanda ke da gwamnati a jihar Kano. Kallon ya koma kan jagororin jam’iyyar domin ganin matakin da za su dauka kan wannan sabon yanayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *