
Gwamnatin Birtaniya ta yi magana kan tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ta yaba da irin ci gaban da aka samu a fannin janyo jari da bunkasa kasuwanci.
Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr. Richard Montgomery, ya bayyana cewa sauye-sauyen da aka yi sun hada da cire tallafin mai da daidaita tsarin canjin kudin waje, wanda hakan ke inganta shigar da jari daga kasashen waje.
Montgomery ya jinjina wa jajircewar gwamnatin Najeriya, yana mai cewa wadannan tsare-tsare suna da muhimmanci wajen bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar. Ya kuma bayyana cewa, duk da cewa wasu daga cikin wadannan sauye-sauyen suna da wahala ga talakawa, suna da tabbacin cewa nan gaba za a ga saukin hauhawar farashi.
A karkashin yarjejeniyar hadin gwiwar kasuwanci ta ETIP da aka kulla tsakanin Najeriya da Birtaniya, kasashen biyu na aiki tare a bangarori guda takwas, ciki har da noma da lafiya. Wannan yarjejeniya na nufin inganta hadin gwiwar tattalin arziki da saukaka dokokin kasuwanci tsakanin kasashen.
Montgomery ya bayyana wasu sabbin zuba jari da gwamnatin Birtaniya ta yi a Najeriya, ciki har da $40.5m a bangarori da dama. Wannan yana nuna karfin gwiwar Birtaniya akan ci gaban Najeriya a fannin tattalin arziki.