
Gwamnatin Tinubu ta sanar da ci gaba da aikin haƙar man fetur a yankin Kolmani, wanda ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe. Sabon shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana cewa za a dawo da aikin da aka dakatar tun bayan gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cikin wata tattaunawa da gidan rediyon BBC Hausa, Ojulari ya bayyana cewa wannan aikin zai haifar da ci gaba a Arewa, tare da bude sababbin hanyoyin samun aiki da farfaɗo da tsofaffin masana’antu. Ya jaddada cewa aikin haƙar man zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin yankin.
Bayo Ojulari ya kuma yi bayani kan shirin kammala wasu muhimman ayyuka na bututun man gas daga Ajaokuta zuwa Kano, wanda zai kara inganta harkokin sufuri da kasuwanci a Arewa.
Wannan al’amari ya zo a lokacin da ‘yan Najeriya ke fuskantar tsadar rayuwa, musamman bayan cire tallafin mai da aka sanar a ranar rantsar da shugaban kasa Bola Tinubu. Ojulari ya bayyana cewa aikin haƙo man zai rage farashin sufuri da kuma inganta tattalin arzikin al’umma.
Gwamnati ta bayyana cewa wannan shiri na haƙar man fetur a Kolmani zai ba da damar inganta rayuwar al’umma da rage talauci a ƙasar.