
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana damuwarsa kan yawaitar amfani da magungunan shaye-shaye a tsakanin matasan Arewacin Najeriya. A wani taron liyafa da aka gudanar a jihar, Uba Sani ya nuna cewa magungunan kamar tramadol da codeine suna zama babbar barazana ga lafiyar al’umma da zaman lafiya a yankin.
Gwamnan ya bayyana cewa binciken Hukumar Kula da Miyagun Kwayoyi ta Duniya (UNODC) na shekarar 2018 ya nuna cewa mutum daya cikin bakwai a Najeriya na amfani da miyagun kwayoyi, inda alƙaluman suka fi yawa a Arewa maso Yamma. Wannan ya jaddada bukatar daukar matakai masu inganci don rage wannan matsala.
Uba Sani ya yi kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki a fannin lafiya da su hada kai wajen samar da ingantaccen shiri na wayar da kan jama’a game da illolin shaye-shaye da kuma yadda za a magance su.
“Yawaitar amfani da magungunan opioid kamar tramadol da codeine na haifar da barazana ga lafiyar matasa, tsaro, da ci gaban yankin,” in ji Uba Sani. Ya kuma yaba wa shugabannin ƙungiyar Pharmacists Society of Nigeria (PSN) bisa kokarinsu na inganta lafiyar jama’a.
Gwamnan ya kara da cewa: “Haɗin gwiwar gwamnati da masana harkar magani na da matukar muhimmanci wajen samar da ingantacciyar lafiya a jihar Kaduna da Najeriya baki ɗaya.”
Wannan jawabi na Gwamna Uba Sani ya zo a lokacin da ake bukatar a dauki matakai na gaggawa don magance matsalar shaye-shaye da ke addabar matasan Arewa.