Dogaran Sarkin Katsina Sun Fasa Ƙofa a Bikin Ɗiyar Gwamna Dikko Raɗɗa

Wani karamin rikici ya faru a wurin bikin auren ɗiyar Gwamna Dikko Raɗɗa a Katsina, lokacin da dogaran sarkin Katsina suka fasa gilashin ƙofar shiga ɗakin taron. Lamarin ya faru ne saboda jinkirin da aka samu kafin a buɗe wa sarkin ƙofar ya shiga.

Bikin ɗaurin auren, wanda ya gudana a gidan gwamnatin Katsina, ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen jihar, har da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun bayyana cewa, lokacin da sarkin ya iso, sai aka samu jinkiri kafin a ba shi damar shiga wurin. Hakan ya fusata dogaransa, suka fasa gilashin ƙofar.

Jami’an tsaro sun rufe ƙofar ne saboda tsauraran matakan tsaro na ofishin shugaban ƙasa, amma daga bisani dogaran sarki suka fasa ƙofar domin mai martaba ya shiga.

Duk da faruwar lamarin, an ci gaba da harkokin bikin lami lafiya, inda shugaban ƙasa Tinubu, Gwamna Radda da sauran manyan baki suka yi addu’a da fatan alheri ga ma’auratan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *