
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gano matsalar da ta addabi Najeriya, wato rashin tsaro, kuma ya yi alkawarin daukar matakan da suka dace don magance matsalar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wajen liyafar cin abincin dare da aka shirya a gidan gwamnatin jihar Katsina, a ziyararsa ta baya-bayan nan zuwa jihar. Ya ce rashin tsaro ya zama babban kalubale ga kasar nan, kuma gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an magance matsalar.
Shugaban kasar ya yi alkawarin zuba jari a fannin fasaha domin kwato dazukan da ke Arewa maso Yammacin Najeriya daga hannun ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane. Ya ce gwamnati za ta yi aiki tare da jihohi da kananan hukumomi don ganin an magance matsalar.
Tinubu ya kuma ce dole ne a magance matsalar rashin tsaro idan har ana son jawo masu zuba hannun jari a Najeriya. Ya ce masu zuba hannun jari ba za su je wuraren da ake fama da ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga ba.
A wani labarin kuma, Shugaba Tinubu ya yabawa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, bisa gaskiyarsa, rikon amana da jajircewarsa wajen sauke nauyin da ke kansa na mulkar mutanen Katsina. Ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da taimakawa Gwamna Radda domin cigaba da ayyukan da yake yi a Katsina.