Wike Ya Yi Allah Wadai da Abin da Ya Faru a Taron Matar Tinubu a Rivers, Ya Zargi Fubara

Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya nuna matuƙar ɓacin ransa game da abin da ya faru a wajen taron da matar shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta shirya a jihar, inda wasu mata suka fice daga wurin suna zanga-zanga.

Wike, wanda a yanzu haka ke aikin gwamnati a Abuja, ya zargi gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da hannu a wannan lamari, yana mai cewa hakan rashin girmamawa ne ga ofishin shugaban ƙasa.

A cikin wata sanarwa da hadiminsa, Lere Olayinka, ya fitar, Wike ya nemi afuwar shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa abin da ya faru, yana mai cewa hakan ba halayyar mutanen jihar Rivers ba ne.

Ya kuma shawarci gwamna Fubara da ya bayyana wa shugaban ƙasa buƙatunsa kai tsaye, maimakon yin wasa da hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *