
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayar da umarnin fitar da N3.8 biliyan domin biyan ƴan fansho haƙƙoƙinsu. Wannan mataki ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen tsofaffin ma’aikata da iyalan ma’aikatan da suka rasu, wadanda ke fama da matsaloli a wajen karɓar haƙƙoƙinsu.
Uba Sani ya bayyana cewa yana ƙudurin faranta ran tsofaffin ma’aikata waɗanda suka yi wa jihar Kaduna hidima. A cewar sanarwar da babban sakataren watsa labarai na gwamnan, Malam Ibraheem Musa, wannan shawara ta fito ne saboda tausayi da kuma halin da tsofaffin ma’aikatan ke ciki.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa aikin tantancewar da ake yi na nufin kawar da masu karɓar fansho na bogi domin tabbatar da cewa kuɗin fansho na gaskiya suna karɓa ba tare da tangarɗa ba. Wannan mataki na nuna ƙudurin gwamnatinsa na tallafa wa tsofaffin ma’aikata da suka ajiye aiki.